10 Faburairu 2016 - 18:01
Iran: Rasha Za Ta Fara Mikawa Iran Makami Mai Linzamin Nan Na S-300

Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Husain Dehqan ya bayyana cewar nan ba da jimawa ba kasar Rasha za ta mika wa Iran kashin farko na makami mai linzamin nan samfurin S-3000

Birgediya Janar Dehqan ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Iran inda ya ce bisa yarjejeniyar sayen makamin da aka kulla tsakanin Iran da kasar Rashan, kasar Rashan za ta ba wa Iran wannan makamin ne a kashi biyu, wanda a halin yanzu an gama shirya kason farko na makamin don dauko shi zuwa Iran, yana mai cewa a tsakiyar shekaran nan ta 2016 ne za a karbi kashi na biyu na makamin.

A watan Nuwamban shekarar bara ta 2015 ne kasar Rashan ta sanar da cewa ta sanya hannu kan yarjejeniyar sayar wa Iran da wannan makami na zamani kirar kasar Rasha a kokarin da Iran din take yi na kara karfafa tsaron kasarta daga hare-haren makiya.

Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila da wasu kawayensu na kasashen Larabawa dai sun jima suna ta kai gwauro su kai mari wajen ganin sun yi kafar ungulu da hana kasar Rasha sayar wa Iran da wannan makamin.288